kamfanin dillancin labaran na Ahlul-Baiti{a.s}-Abna- a la’asar din juma’a ne aka bude gasara karatun kur’ani ta duniya da ake yi da karatun kur’ani mai girma da kwararren mai karatun nan na kasa “Ja’afar Fard” ya bude, da halartar baki makaranta na ciki da waje da wasu manyan shugabannin kasa a zauren taro na kasa dake Tehran.
Zuwa yanzu dai daga wadanda suka halarata akwai mai bayar da shawara ga kwamandan kasa na baki daya “Rahim Safawi” da kuma ministan shiryarwa “Ali Jannati” da kuma shugaban kwamitin shahidai da sadaukarwa “Hujjatul islam shaheedi’ da shugaban kwamitin ofishin shugaban kasa “Dr Nahawand”, da duka suka halarta.
Akwai batun halarata shugaban kasa “Hassan Rohani” a cikin tsarin bude wannan taro da Ali Muhammadi shugaban ofishin waqafi da ayyukan alherai, da bayanan bude taron.
Haka nan ma akwai wasu tsarurrukan da za a gabatar da sunan “Heme Ma’arifat” wato Heman Ilimi da suka hada da “Hame waqif bosheem” da yake nufin dukkanmu mun miqe tsaye, hada da bude neman gudummuwa da tarayya cikin gina asibitin Kansa, da shawarar iyali, da hardar kur’ani, da bangaren bayar da shawarar tarbiyyar yara. Sannan a dakin litattafai ma akwai littattfan addini da ilimi da za a kawo don samun masu bukata.ABNA