kamfanin dillanci labaran na Ahlul-Baiti{a.s}- Abna- shugaban wakafi da ayyukan alherai ne bayan ya yi maraba da zuwa ga masu halartar taro da ya hada da shugaban kasa, ministan shiryarwa, shugaban cibiyar shahidai da ayyukan sadaukarwa, ambasadodin kasashen musulmi, masu kula da bangaren kur’ani da sauran mahalarta. Ya kuma tunatar da cewa littafin Allah shi ne ambato da wa’azi ga dan adam, kuma ubangiji ya sanar da wannan a matsayin haske da ya sauka tare da zuwan annabi (s.a.w).
Hujjatul islam Ali Muhammadi yana cewa: Duk wanda ya kasance tare da littafin sama to yana cikin rabauta da arzutar duniya da lahira ko da kuwa bai fahimci kur’anin ba, ya ce: baki daga kasashe 85 ne suka halarci wannan gasar ta talatin da biyu daga sasannin duniya biyar a matsayin masu wakilata mahardatan kur’ani mai daraja a wannan taron mai haske da zasu zuba cikin sati guda.
Sannan ya yi nuni da cewa a gefen gasar akwai abin da ya shafin tsarin mas’alolin da suka shafi yara da samari. Kamar yadda ya yi nuni da cewa zuwa yanzu an aiko kusan sama da makaloli 700 zuwa ga ofishin gudanarwa. Kuma daga karshe za a karrama mata bakwai daga masu ayyukan kur’ani na duniya.ABNA