kamfanin dillancin labaran na Ahlul-Baiti{a.s}-Abna- kungiyoyin bege ne da suka hada da, Mi’ad, Mi’iraj, Baqiyyatullah, suka halarci taron daga birinin Qum da suka yi yabo da bege a wurin bude taron.
Shugaban masu begen Mi’iraj yana cewa wannan jama’ar da ta shahara an kafa ta ne a matsayin jama’ar da take yabon ma’asuma a birnin Qum da ta fara ayyukanta tun shekarar 1392 H.Sh.
Haka nan ma sayyid Muhammad Mujani yana kawo cewa an gabatar da wannan yabon da begen a shekarun 92, 93, haka nan ma yanzu an halarta ne da yardar masu gudanarwa a wannan shekarar.
Ya kara da cewa kusan wata daya ke nan aka samu shirin yin haka da yarda masu gudanarwa da kula da gasar karatun kur’ani na “sazimane auqaf” domin yin wannan begen; kuma an zavi waqar “Taha” da aka yi gwajinta kusan sau 20 sannan aka gabatar da ita ta hannun masu begen “Alqudwa” a bude wannan taron.ABNA