26 Afirilu 2020 - 06:15
Rauhani: Iran Tana Sa Ido Akan Duk Wani Kai Da Komowar Amurka A Cikin Wannan Yankin

Shugaban kasar ta Iran wanda ya tattauna ta wayar tarho da sarkin kasar Qatar, Sheikh Tamim Bin Hamad ali-Thani, ya jaddada muhimmancin ganin kasashe sun rubanya kokarinsu domin tabbatar da zaman lafiya da kwanciyar hankali a cikin wannan yankin

(ABNA24.com) Shugaban kasar na Iran ya taya sarkin Qatar murnar shigowar watan azumin Ramadan mai alfarma, tare da yin addu’ar Allah ya albarkaci al’ummar musulmi da falalar da ke cikin watan mai alfarma.

Da yake Magana akan halayyar Amurka acikin wannan yankin, shugaban kasar ta Iran ya ce; Jamhuriyar musulunci ta Iran tana sa ido da bin diddigin duk wani motsin Amurka, amma tabbas,mu ba za mu zama masu tsokana ba.

A nashi gefen, sarkin Qatar ya bayyana fatansa na ganin kasashen biyu sun yi aiki domin tabbatar da zaman lafiya a cikin wannan yankin.


/129