ABNA24 : Shugaba Rauhani ya bayyana hakan ne a lokacin da yake halartar zaman majalisar ministocin kasar a birnin Tehran, inda ya bayyana cewa kasancewar Iran a cikin wannan yarjejeniya yana da muhimmanci ga dukkanin bangarorin da suka rattaba hannu a kanta.
Ya ce masu cewa Iran ta dawo a cikin yarjejeniyar nukiliya suna yin kure, domin kuwa Iran ba ta fice daga cikin wannan yarjejeniya, ta dai jingine yin aiki da wasu bangarorin yarjejeniyar ne kawai, har zuwa lokacin da za a janye takunkuman da aka kakaba mata, wanda hakan ya sabawa yarjejeniyar.
Ya ci gaba da cewa, manyan kasashen turai uku wato Burtaniya, Jamus da kuma Faransa, ba su cika alkawullan da suka daukar wa Iran ba, saboda haka ba su da hakkin yin wasu kalamai na suka a kanta dangane da matakan da ta dauka.
Haka nan kuma ya yi ishara da matakin da kasar ta dauka a jiya, na janye izinin da ta bai wa masu bincike na hukumar IAEA, na kai ziyarar ba-zata a cibiyoyinta na nukiliya a duk lokaci da suka ga dama, inda ya bayyana cewa hakan mataki ne mai kyau, kuma zai taimaka wajen mayar komai a kan tsari.
342/